logo

HAUSA

Tsarin Sin na farfadowa da inganta tattalin arziki bai sauya ba

2023-12-21 19:08:43 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana yayin taron manema labarai na Alhamis din nan cewa, ci gaban kasar Sin na fuskantar karin yanayi mai inganci, sama da nau’o’in kalubalen da yake fuskanta, kuma muhimman matakan da kasar ke aiwatarwa, na farfadowa da inganta tattalin arziki a tsawon lokaci ba su sauya ba, kana dukkanin ginshikai dake goya baya ga samar da ci gaba mai inganci, na haifar da karin kyautatuwar yanayi a fannin.

Kafin hakan, yayin wata ganawa da manema labarai, wakilin asusun ba da lamuni na duniya IMF Steven Alan Barnett, ya ce a shekarar bana, Sin za ta samar da gudummawar kaso 1 bisa 3 na karfin bunkasar tattalin arzikin duniya. Barnett ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin Sin zai ci gaba da bunkasa a shekarar 2024.

Game da hakan, Wang Wenbin ya ce cibiyoyin kasa da kasa masu yawa, ciki har da IMF, da hukumar bunkasa hadin gwiwar raya tattalin arziki da samar da ci gaba, a baya bayan nan sun daga mizanin hasashen su na ci gaban tattalin arzikin Sin, a shekarar nan ta bana, da ma shekarar dake tafe. Hakan a cewarsa na nuna cewa, Sin ta zama babban jigo dake ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya. (Saminu Alhassan)