logo

HAUSA

Firaministan Sin ya jaddada bukatar kyautata yanayin kasuwanci da kara habaka kasuwanni

2023-12-21 10:54:30 CMG

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya jaddada bukatar samar da wani yanayi na kasuwanci mai inganci, da ya dace da yanayin kasuwa, mai martaba doka da oda, da zama na kasa da kasa, don sa kaimi ga samun bunkasuwa mai inganci a kasar Sin, ta yadda za a kara kuzarin kasuwanni a ko da yaushe..

Li ya bayyana, yayin wani zaman nazari da majalisar gudanarwar kasar ta shirya cewa, kyautata yanayin kasuwanci na da matukar muhimmanci, wajen kara karfin kasuwanni, da kara samun bunkasuwa

Ya ce, a cikin matakan da aka dauka don cimma wannan buri, za a kara yin kokari wajen kiyaye takarar kasuwa bisa adalci, da kawar da ka'idoji da ayyukan da ke kawo cikas ga hadewar kasuwanni, da yin takara mai tsafta, don tabbatar da cewa, dukkan nau’o’in kamfanoni sun shiga takara bisa adalci, da kara kare hakkoki da moriyar dukkan nau’o’in kasuwanci.(Ibrahim)