logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Sin ya zanta da takwaransa na kasar Philippines ta wayar tarho

2023-12-21 14:34:41 CMG Hausa

Jiya Laraba, mamban hukumar siyara ta kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasa Wang Yi, ya zanta da ministan harkokin wajen kasar Philippines Enrique A. Manalo ta wayar tarho.

A yayin zantawarsu, Wang Yi ya shawarci Philippines da ta kaucewa ci gaba da bin hanya maras dacewa, ta koma kan turba ta gari, musamman ma batun daidaita ayyukan dake shafar harkokin teku. Ya ce a halin da ake ciki, Sin da Philippines su kan ga muhimmin lokaci na daidaita sabanin dake tsakaninsu, don haka ya kamata Philippines ta aiwatar da matakai yadda ya kamata.

Wang ya kara da cewa, idan Philippines ta ci gaba da aikata laifi, ko hada kai da wadanda suke da mugun buri, na ci gaba da haifar da tashe-tashen hankula a kasar Sin, tabbas Sin za ta kare ikonta bisa dokoki, tare da mai da martani ba tare da nuna shakku ko kadan ba. (Maryam)