logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya gana da firaministan kasar Rasha

2023-12-20 14:25:43 CMG

Da safiyar yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da firaministan kasar Rasha Mikhail Vladimirovich Mishustin.

A yayin ganawar, Xi Jinping ya jaddada cewa, karfin juriya, da babbar fa'ida, da kuma kyakkyawan tushen tattalin arzikin Sin na dogon lokaci duk ba su sauya ba. Kasar Sin na tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da ci gaba mai inganci, da kuma kara kyautata bude kofarta ga kasashen ketare, kuma za ta samar da sabbin damammaki ga kasashen da suka hada da Rasha. Kana kamata ya yi kasashen biyu su yi amfani da fifikonsu na amincewa da juna ta fannin siyasa, da taimakon juna a fannin tattalin arziki, da hadewa da juna ta fannin manyan ababen more rayuwa, da ma cudanyar al’ummunsu, su yi ta fadada hadin gwiwarsu, tare da zurfafa hadin gwiwa ta fannonin tattalin arziki, da makamashi, da sadarwa da sauransu, don kiyaye tsarin samar da kayayyaki tare.

A nasa bangaren kuwa, mista Mishustin ya ce, Rasha ta gamsu da bunkasuwar hadin gwiwar kasashen biyu, kuma tana fatan ci gaba da yin kokari tare da kasar Sin, don fadada hadin gwiwa ta fannonin tattalin arziki da makamashi, da kuma sadarwa, tare da karfafa dankon zumunci a tsakanin jama’ar kasashen biyu daga zuriya zuwa zuriya. (Lubabatu)