logo

HAUSA

Sin na godiya bisa sakwannin jaje daga sassan kasa da kasa sakamakon girgizar kasa da ta auku a gundumar Jishishan

2023-12-20 19:14:29 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce kasar sa na matukar godiya bisa yadda sassan kasa da kasa ke ta aiko da sakwannin su na jaje, bisa girgizar kasa da ta auku a gundumar Jishishan ta lardin Gansu na arewa maso yammacin kasar Sin.

Wang, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na Larabar nan, ya ce tuni kasashen Rasha, da Cambodia, da Pakistan, da Afghanistan, da Masar, da Saudiyya, da Isra’ila da sauran su, da ma wasu hukumomin kasa da kasa suka gabatar da sakon ta’aziyya da jaje ga bangaren Sin.

Jami’in ya kara da cewa, a halin da ake ciki, dukkanin jami’an aikin ceto da ake bukata na gudanar da ayyukan ceto bisa tsari, ana kuma shigar da kayayyakin tallafin jin kai, kamar tantuna, da gadajen tafi da gidan ka, da tufafin kare sanyi, zuwa yankunan da girgizar kasar ta shafa.

Da tsakar daren ranar Litinin ne dai girgizar kasa mai karfin maki 6.2 ta auku a gundumar Jishishan ta lardin Gansu, lamarin da ya haifar da rasuwar mutane da dama, tare da jikkatar wasu.  (Saminu Alhassan)