logo

HAUSA

Firaministan Sin da na Rasha sun jagoranci taron firaministocin Sin da Rasha karo na 28

2023-12-20 10:39:37 CMG

A jiya ne, firaministan Sin Li Qiang da takwaransa na Rasha Mikhail Mishustin, suka jagoranci taro karo na 28 tsakanin firaministocin kasashen Sin da Rasha a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Bangarorin biyu sun amince cewa, a halin yanzu, kasashen Sin da Rasha sun kuduri aniyar samun bunkasuwa da farfadowa. Ya kamata bangarorin biyu su kara inganta karfin harkokinsu na cikin gida, don raya dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha, da fadada hadin gwiwar cinikayya da aikin gona, da samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci ta yadda kamfanoninsu za su zuba jari a kasashensu, da kiyaye tsaron makamashin kasashen biyu tare, da karfafa hadin kai, da inganta mu'amala tsakanin ma'aikata, da tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali na masana'antu da tsarin samar da kayayyaki.(Ibrahim)