logo

HAUSA

Girgizar kasa mai karfin maki 5.5 ta afku a birnin Atush na jihar Xinjiang

2023-12-19 16:24:04 CMG Hausa

Da karfe misalin 9 da mintuna 46 na safiyar yau ne, girgizar kasa mai karfin maki 5.5 ta afku a birnin Atush na yankin Kizilsu Kirgiz mai cin gashin kansa na jihar Xinjiang.

Bayan afkuwar girgizar kasar, hukumar ceto ta yankin ta aike da motoci 9 da mutane 30 zuwa inda lamarin ya faru, domin gudanar da bincike. Kawo yanzu ba a samu asarar rayuka ko dukiya ba. (Safiyah Ma)