logo

HAUSA

Sin ta ware kudade Yuan miliyan 250 don tallafawa lardunan Gansu da Qinghai masu fama da tasirin bala’in girgizar kasa

2023-12-19 20:51:30 CGTN HAUSA

 

Kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya bayyana a yau Talata cewa, bayan aukuwar bala’in girgizar kasa a gundumar Jishishan dake yankin Linxia ta lardin Gansu, ya yi amfani da tsarin ko ta kwana nan da nan, don tabbatar da ba da tallafin kwal, da wutar lantarki, da gas, da kuma rarraba kayayyaki cikin gaggawa, da samar da isassun kayayyakin more rayuwa, da tabbatar da farashin yau da kullum.

Ban da wannan kuma, gwamnatin Sin ta ware kudade har Yuan miliyan 250, daga cikin kasafin kudin kwamitin tsakiya ga lardunan Gansu da Qinghai, don farfado da manyan ababen more rayuwa, da na’urorin hidimmar wurare cikin sauri.

Hukumar masana’antu da sadarwa ta kasar ta ba labari a wannan rana cewa, bala’in ya haddasa lalacewar na’urorin sadarwa a wadannan larduna biyu. Bayan aikin gyarawa cikin gaggawa da hukumar ta yi, ya zuwa karfe 2 na yammacin yau Talata, an maido da tasoshi 279 daga cikin 314 da suka lalace, kuma an maido da layukan sadarwa 2, matakin da ya bayar da damar gudanar da harkokin sadarwa a wuraren da bala’in ya ritsa da su yadda ya kamata.(Amina Xu)