logo

HAUSA

Xi ya taya Al-Sisi murnar lashe zaben shugabancin Masar

2023-12-19 19:15:43 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taya shugaban Masar Abdel-Fattah Al-Sisi, murnar sake zaben sa da aka yi a matsayin shugaban kasar Masar.

Cikin sakon taya murnar da ya aikewa Al-Sisi a Talatar nan, shugaba Xi ya ce Sin da Masar abokai ne na kusa, wadanda ke da mahanga daya, kuma sun aminta da juna, kana abokan hulda na hakika dake aiki tare, wajen ingiza ci gaban bai daya.

Ya ce a shekarun baya bayan nan, alakar Sin da Masar tana kara bunkasa, suna gudanar da hadin gwiwa a fannoni daban daban, wanda hakan ya haifar da kyakkyawan sakamako, yayin da abota tsakanin al’ummun su ke kara zurfafa.

Daga nan sai shugaba Xi ya ce yana dora muhimmancin gaske, ga ci gaban dangantakar Sin da Masar, kana a shirye yake ya yi aiki tare da shugaba Al-Sisi, wajen ingiza goyon bayan juna, da hadin gwiwar Sin da Masar ta fuskar raya shawarar ziri daya da hanya daya, da aiki tare wajen kare moriyar bai daya ta daukacin kasashe masu tasowa, da ci gaba da daga matsayin cikakkiyar hadin gwiwarsu bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, ta yadda hakan zai amfani al’ummun kasashen 2. (Saminu Alhassan)