logo

HAUSA

Sirrin Ci Gaban Kasar Sin: Daga Yin Kwaskwarima Da Bude Kofa Zuwa Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa

2023-12-19 15:42:56 CMG Hausa

Shekaru 45 da suka gabata, yawan kudin shigar kowa ne dan kasar Sin, dalar Amurka 190 ne kacal, wanda hakan ya sa ta kasance cikin kasashe mafi karancin ci gaba a duniya. Jimillar yawan shigi da ficin kayayyaki, fiye da dalar Amurka biliyan 20 ne kawai, kuma amfani da jarin waje ba komai ba ne. Yayin da ake fuskantar irin wannan yanayi, shugaban Sin na lokacin Deng Xiaoping ya yanke shawarar aiwatar da manufar yin "gyare-gyare da bude kofa ga waje". Mene ne gyare-gyare? Deng Xiaoping ya yi nuni da cewa, "gyare-gyare shi ne 'yantar da sassan da suka dace." Mene ne bude kofa? Deng Xiaoping ya ce, "Duniya a yau, duniya ce dake bude kofa, ba zai taba yiwuwa kowace kasa ta ci gaba da zama saniyar ware ba, idan har muna son samun bunkasuwa, tilas ne mu dage wajen bude kofa ga ketare." A karkashin shawarar Deng Xiaoping, an rubuta shirin "yin gyare-gyare da bude kofa ga waje" cikin kundin tsarin mulkin kasar a matsayin muhimmin manufar kasar Sin. Wannan manufa ta taimaka wajen inganta tsarin gurguzu mai sigar kasar Sin, ta kuma canza makomar kasar Sin ta zamani.

Shekaru 10 da suka gabata, a shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yanke shawarar zurfafa yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje. A cikin shekaru 10 da suka gabata, ta hanyar zurfafa yin gyare-gyare, kusan mutane miliyan 100 sun fita daga kangin fatara. A cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta gina tsarin masana'antu na zamani, da sa kaimi ga "juyin -juya hali", da aiwatar da cikakken tsarin mulki bisa jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da kuma yaki da cin hanci da rashawa, da kafa tsarin makomar Sin. 

A shekarar 2022, kasar Sin ta bayyana cikakken zurfafa yin gyare-gyare a matsayin wani muhimmin abin da zai sa kasar Sin ta inganta hanyar zamanantarwa da farfado da kasa.

Kara zurfafa gyare-gyare a lokaci guda cikin sauri, shi ne babban matakin bude kofa ga kasashen waje. Xi ya yi imanin cewa, bude kofa yana kawo ci gaba, yayin da rufe kofa yana haifar da koma baya. A cikin shekaru 10 da suka gabata, Xi ya ba da shawarar yin hadin gwiwa wajen raya shawarar "Ziri daya da hanya daya", kuma fiye da kasashe 150 da kungiyoyin kasa da kasa 30 sun rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa fiye da 230. Kasar Sin ta kafa yankuna ko tasoshin ruwa na ciniki cikin 'yanci 23. Kasar Sin ta shirya bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin na farko a duniya, da baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa, da baje kolin inganta tsarin samar da kayayyaki na duniya.

Tun bayan da aka aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, yawan gudummawar da kasar Sin ta bayar ga ci gaban tattalin arzikin duniya, ya zarce kashi 30 cikin 100 cikin shekaru masu yawa. Kasashen da suka ci gaba da masu tasowa, sun amfana matuka daga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, wanda hakan ya kara azama kan tattalin arzikin duniya. (Ibrahim Yaya)