logo

HAUSA

Sin na matukar adawa da sukar da Amurka ke yiwa dokar tsaron kasa ta HK da batun sayarwa Taiwan makamai

2023-12-18 18:59:15 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin na matukar adawa da yadda Amurka ke sukar lamirin dokar tsaron kasa ta yankin musamman na HK, da yadda take tsoma baki a batun dokokin yankin.

Wang Wenbin ya bayyana matsayar kasar ta Sin ne a Litinin din nan, yayin da yake mayar da martani ga kalaman sakataren wajen Amurka Antony Blinken, don gane da yankin na HK.

Game da matsayar ma’aikatar wajen Amurka, ta amincewa da sayarwa yankin Taiwan na kasar Sin makamai kuwa, Wang Wenbin ya ce Sin na matukar bayyana bacin rai game da hakan, kuma tana adawa da matakin, kana za ta gabatar da korafin ta ga tsagin na Amurka. Kaza lika Sin za ta aiwatar da matakan maida martani, kan kamfanonin dake da hannu cikin batun sayarwa yankin na Taiwan makamai. (Saminu Alhassan)