logo

HAUSA

Xi ya taya sabon sarkin Kuwait murna

2023-12-18 13:55:15 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon taya murna ga sabon sarkin Kuwait, Sheikh Mishal Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah, tare da yin alkawarin yin aikin tare, don kara inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Xi ya ce, yana mai da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da Sheikh Mishal, wajen daukaka dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Kuwait, ta yadda za a samar da karin moriya ga jama'ar kasashen biyu.(Ibrahim)