logo

HAUSA

Firaministan Rasha zai halarci taro na 28 na shugabannin gwamnatocin Sin da Rasha

2023-12-18 18:44:51 CMG Hausa

Bisa gayyatar da firaministan kasar Sin Li Qiang ya yi masa, firaministan Rasha Mikhail Mishustin, zai halarci taro karo na 28, na shugabannin gwamnatocin Sin da Rasha, wanda zai gudana tsakanin 19 zuwa 20 ga watan nan na Disamba, kamar dai yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya sanar a Litinin din nan.   (Saminu Alhassan)