logo

HAUSA

Adadin masu kamuwa da cutar numfashi ya ragu a Sin

2023-12-17 16:33:43 CMG Hausa

A yau Lahadi 17 ga wata ne hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin, ta kira taron ganawa da manema labarai, inda aka yi bayani game da yanayin kandagarkin cutar numfashi da kasar ke ciki a lokacin sanyi.

Yayin taron, kakakin hukumar Mi Feng, ya bayyana cewa, a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, adadin masu kamuwa da cutar munfashi dake zuwa asibitoci a fadin kasar ya ragu, kuma asibitocin kasar suna gudanar da ayyukan jinya yadda ya kamata. Ya ce alkaluman sa ido da aka tattara sun nuna cewa, kananan asibitocin wurare daban daban dake fadin kasar, suna kulawa da masu fama da zazzabi har kaso 44 bisa dari, lamarin da ya nuna cewa, ana magance bukatun jinya na masu kamuwa da cutar yadda ya kamata.

Bayan haka, jami’in ya ce akwai bukatar a kara karfafa aikin sa ido a aikin jinyar cutar numfashi, da kuma tantance yanayin da ake ciki a bangaren, ta yadda za a yi amfani da albarkatun likitanci yadda ya kamata, tare kuma da kyautata hidimomin asibitoci. A sa’i daya kuma, ya dace a yi amfani da fifikon maganin gargajiyar kasar Sin, wajen tabbatar da bukatun masu fama da cutar. (Jamila)