logo

HAUSA

Xi ya aike da sakon ta’aziyya ga sabon sarkin masarautar Kuwait bisa rasuwar sarki Nawaf Al-Sabah

2023-12-17 20:08:03 CMG Hausa

A yau Lahadi 17 ga wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta’aziyya ga sabon sarkin masarautar Kuwait Mishal Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah, game da rasuwar sarki Nawaf Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah, inda cikin sakon na sa ya bayyana matukar alhini, a madadin gwamnati da al’ummar kasar Sin, tare da isar da sakon jaje ga iyalan sarki Nawaf da al’ummar kasar Kuwait.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, al’ummar Kuwait suna kaunar sarki Nawaf, wanda ya taka rawar gani a fannin bunkasa ci gaban huldar dake tsakanin kasar Sin da Kuwait, don haka rasuwarsa babbar hasara ce ga al’ummar kasarsa, yayin da al’ummar Sinawa su ma suka rasa tsohon aboki.

Shugaban na Sin ya kara da cewa a ko da yaushe, gwamnatin kasar Sin da al’ummar kasar suna darajanta zumunta dake tsakaninsu da Kuwait, kuma a nan gaba, hulda tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da bunkasa yadda ya kamata bisa kokarin sassan biyu. (Jamila)