logo

HAUSA

Sin ta zartas da dokar sanya ido da jagorancin cibiyoyin hada hadar biyan kudade da ba na banki ba

2023-12-17 16:30:25 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya sanya hannu kan wata doka ta majalissar gudanarwar kasar Sin, wadda za ta fayyace ka’idojin sanya ido, da jagorancin cibiyoyin hada hadar biyan kudade da ba na banki ba, wadda za ta fara aiki tun daga ranar 1 ga watan Mayun shekarar 2024.

Dokokin dake kunshe cikin dokar za su bayar da kariyar doka, game da ayyukan sanya ido, da jagorancin irin wadannan cibiyoyi, da yadda suke gudanar da kasuwanci, da ingiza bunkasar su yadda ya kamata, da kare hakkoki da moriyar abokan huldar su, da taimakawa cibiyoyin, ta yadda za su iya sauke nauyin dake wuyan su na raya tattalin arziki, da biyan bukatun abokan huldar su na fadada hanyoyin biyan kudade.

Sabbin dokokin sun fayyace ma’anar cibiyoyin hada-hadar kudi da ba bankuna ba ne, da abubuwan da ake bukata kafin kafuwar su, da dokokin kyautata tsarin biyan kudade ta karkashin su.

Kaza lika an tanadi cewa, domin kare hakkokin doka na abokan hulda, wajibi ne wadannan cibiyoyi su kafa tsarin sanya ido, da na kandagarkin asara. Har ila yau, su tabbatar da tsaron asusun jama’a daga maha’inta, kamar masu kafa gidauniyar bogi, da ‘yan damfara ta yanar gizo, da masu safarar kudade, da ‘yan caca, da sauran masu aikata laifuka.

A daya bangaren kuma, dokokin sun fayyace babban bankin Sin a matsayin wanda ke da nauyin doka, na lura da tsara dabarun kandagarkin hadurra, ga wadannan cibiyoyi da ba bankuna ba, kana an umarci kananan hukumomi da su yi hadin gwiwa da babban bankin kasa, wajen kandagarkin asarori da ka iya bullowa karkashin hada hadar cibiyoyin. (Saminu Alhassan)