logo

HAUSA

Tsohon shugaban Habasha: ya kamata a yi koyi da kasar Sin da mai da hankali ga bukatun jama’a

2023-12-16 15:57:49 CMG Hausa

Tsohon shugaban kasar Habasha Mulatu Teshome, ya bayyana wa wakiliyar babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG a kwanakin baya cewa, ya kamata kasarsa ta Habasha, ta yi koyi da kasar Sin, wajen aiwatar da ayyuka bisa hakikanin yanayin da ake ciki, da mai da hankali ga bukatun jama’a.

Ya ce, ya kamata a mai da hankali ga moriyar jama’a, yayin da aka tsara shirye-shirye don tabbatar da moriyar jama’a daga kwaskwarimar da ake yi. Ya ce idan jama’a ba su samu moriya ba, ko kuma ba a daidaita matsalar talauci ba, ba za a iya cimma nasarar yin kwaskwarima ba. Kana idan jama’a sun samu moriya daga kwaskwarimar da aka yi, da kuma aikin zamanintar da kasa, hakan zai sa su goyi bayan gwamnatin kasarsu, su kuma yi kokari tare da gwamnatin.

Game da ra’ayin tarkon basussuka da wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suke bayyanawa, Mulatu Teshome ya bayyana cewa, bai amincewa da wannan ra’ayi ba. Ya ce akwai wasu mutanen dake fadin hakan, amma ba sa samar da kudi ko kadan ga nahiyar Afirka, musamman don gudanar da manyan ayyukan gina hanyoyin motoci, da jiragen kasa, da tasoshin jiragen ruwa. Sin na samar da kudaden ga kasashen Afirka, sai ga shi wadancan mutane suna cewa, kasashen nahiyar za su fuskanci tarkon basussuka. Ya kara da cewa, basussuka ne a halin yanzu, amma a nan gaba, za a samu riba daga ayyukan da aka gudanar da su. (Zainab)