logo

HAUSA

Wang Yi Ya Gana Da Manyan Jami’an Saudiyya Da Iran

2023-12-16 15:50:32 CMG Hausa

Mambar ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Wang Yi, ya gana da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Waleed Elkhereiji, da mataimakin ministan harkokin waje mai lura da harkokin siyasa na kasar Iran Ali Bagheri Kani, jiya Jumma’a a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Manyan bakin sun iso kasar Sin ne domin gudanar da taron farko, na kwamitin hadin kan kasashen Sin da Saudiyya da Iran.

Cikin jawabinsa yayin taron, mista Wang, wanda kuma shi ne daraktan hukumar lura da harkokin waje, ta kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya ce har kullum kasar Sin na goyon bayan al’ummun yankin Gabas ta Tsakiya, a kokarinsu na lalubo hanyar samar da ci gaba mai zaman kanta. Kaza lika, tana goyon bayan kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, game da burinsu na yin aiki tare, don warware matsalolin tsaro dake addabar yankinsu, kana tana goyon bayan Saudiyya da Iran, game da kokarinsu na ci gaba da ingiza matakan bunkasa dangantaka.

Wang ya kara da cewa, Sin ta sha alwashin amfani da wannan taro wajen ingiza kawance na makwaftaka tsakanin Saudiyya da Iran, tare da ba da sabbin gudummawa ga bunkasa zaman lafiya da daidaito a Gabas ta Tsakiya.

Yayin taron sassan 3, manyan jami’an Saudiyya da Iran, sun bayyana burinsu na mara baya ga aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar Beijing. Yayin da ita kuma Sin ta jaddada aniyarta, ta taka muhimmiyar rawa, da goyon bayan Saudiyya da Iran, wajen ci gaba da aiwatar da matakan karfafa dangantaka.  (Saminu Alhassan)