logo

HAUSA

Xi ya yi rangadi a birnin Laibin na jihar Guangxi

2023-12-15 10:13:02 CMG Hausa

Sakataren kwamitin koli na JKS, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a birnin Laibin dake jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai.

Yayin ziyarar gani da ido da shugaban na Sin ya gudanar da yammaci jiya Alhamis, ya isa cibiyar tattara rake, da kamfanin sarrafa sukari dake birnin, ya kuma ganewa idanun sa yadda ake renon iri, da shuka, da girbin rake, da ma yadda ake bunkasa masana’antar yin sukari. (Saminu Alhassan)