logo

HAUSA

Sin ta yabawa ra’ayin shugaban Rasha kan dangantakar dake tsakanin Rasha da Sin

2023-12-15 20:23:07 CMG Hausa

S

hugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana a kwanakin baya cewa, hadin gwiwa tsakanin Rasha da Sin ya kai matsayin da ba a taba ganin irinsa ba. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, kasar Sin ta lura da kyawawan kalaman da shugaba Putin ya yi kan dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha, kuma ta yaba da hakan. Bisa manufofin da shugabannin kasashen biyu suka tsara, dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ta samu ci gaba yadda ya kamata. Bangarorin biyu sun kiyaye ka’idojin zama ‘yan ba-ruwanmu, da rashin nuna adawa da juna, da rashin nuna adawa da saura, kana bisa tushen girmamawa juna da yin zaman daidai wa daida da samun moriyar juna, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da hadin gwiwarsu a fannoni daban daban sun inganta, wadanda suka amfanawa jama’ar kasashen biyu, tare da taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga samun bunkasuwa tare a duniya baki daya. Mao Ning ta kara da cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ta zarce tsarin kawancen siyasa da soja na lokacin yakin cacar baka, kana ta bambanta da kawancen kungiyar NATO da ra’ayin nuna adawa a tsakanin kungiyoyi daban daban.

Game da dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka, Mao Ning ta bayyana cewa, Sin ta yi imanin cewa, raya dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata zai kawo moriya ga kasashen biyu har ma ga duniya baki daya. Sin tana fatan kasar Amurka za ta cika alkawarinta, kuma bai kamata Amurka ta yanke hulda da saka takunkumi ga kamfanonin kasar Sin yayin da take jaddada yin hadin gwiwa tare da kasar Sin ba. (Zainab)