logo

HAUSA

Kasafin Kudin Shiga Na Gwamnatin Sin Ya Karu Da 7.9% A Watan Janairu Zuwa Nuwamba

2023-12-15 20:26:10 CMG Hausa

Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, yawan kasafin kudin shiga da gwamnatin Sin ke samu ya karu da kashi 7.9 bisa 100 bisa makamancin lokaci na bara, zuwa kudin Sin RMB yuan triliyan 20.01, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 2.82 a cikin watanni 11 na farkon shekarar 2023.

Baki daya, kudaden shiga na kasafin kudi, yana nufin kudin shiga da gwamnati ke samu, ta hanyar shiga a dama da ita wajen rarraba kayayyakin zamantakewa. Wannan wani tabbaci ne a bangaren kudi don tabbatar da tafiyar da aikin gwamnati. (Ibrahim)