logo

HAUSA

Sin Ta Gina Cibiyoyin Fasahar Aikin Gona Na Gwaji Guda 24 A Afirka

2023-12-15 19:20:30 CMG Hausa

A wani taron manema labarai na musamman da hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin ta gudanar yau Jumma’a, jami'an da abin ya shafa sun bayyana cewa, kasashe 52 daga cikin kasashen Afirka 53 da suka kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin, sun sanya hannu kan takardun hadin gwiwa da kasar Sin don raya “shawarar Ziri Daya da Hanya Daya", inda suka yi nasarar kammala manyan ayyuka da "kanana da kyawawan ayyuka" wadanda suka taimaka wajen inganta rayuwa, da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar jama’a a kasashen Afirka.

Xu Jianping, darektan sashen bude kofa na hukumar raya kasa da yin garambawul ta kasar Sin ya bayyana cewa, manyan ayyukan injiniya da dama, irin su layin dogo na Mombasa zuwa Nairobi na kasar Kenya, da tashar jiragen ruwa na Lekki dake Najeriya, sun inganta kayayyakin more rayuwa a Afirka yadda ya kamata. A fannin rage talauci da amfanar jama'a kuwa, kasar Sin ta kafa cibiyoyin fasahar aikin gona na gwaji guda 24 a Afirka, da inganta fasahohin zamani sama da 300 da ake amfani da su kamar shuka masara da aka tagwaita, da karuwar yawan amfanin gona da kashi 30 zuwa 60 cikin 100, matakin da ya taimakawa kasashen Afirka inganta matakan bunkasa aikin gona. Haka kuma, da dama daga cikin "kanana kuma kyawawan ayyukan" na inganta rayuwa, irin su "cibiyar koyon sana’o’i ta Luban" sun taimaka wajen inganta rayuwar jama'a a kasashen Afirka.(Ibrahim)