logo

HAUSA

Xi Ya Yi Musayar Sakon Taya Murna Da Takwaransa Na Kenya Kan Cika Shekaru 60 Da Kulla Huldar Diplomasiyya Tsakanin Sin Da Kenya

2023-12-14 20:05:38 CMG Hausa

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi musayar sakon taya murna da takwaransa na kasar Kenya William Ruto, domin murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Xi ya bayyana aniyarsa ta yin aiki tare da shugaba William Ruto, ta hanyar amfani da bikin cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, a matsayin wani sabon mafari, don kama turbar inganta hadin gwiwa ta musamman wajen samun ci gaba da farfado da kasashensu.

A nasa bangare kuwa, shugaba Ruto ya bayyana cewa, kasar Kenya na son yin aiki tare da kasar Sin, wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa karo na uku kan “shawarar Ziri Daya da Hanya Daya”, da kuma taron shugabannin kasashen Sin da Afirka da aka yi a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, ta yadda za a samar da makoma mai haske ta samun ci gaba mai dorewa, da wadata, da sada zumunci, ci gaban bai daya a hadin gwiwar kasashen biyu. (Ibrahim)