logo

HAUSA

Wang Yi: Ziyarar Da Xi Ya Kai Vietnam Ta Samu Gagarumar Nasara

2023-12-14 20:47:44 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana Alhamis din nan cewa, ziyarar da babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai kasar Vietnam, batun siyasa ne mafi muhimmanci a alakar dake tsakanin kasashen Sin da Vietnam a wannan shekara, kuma ta samu gagarumar nasara.

Wang, mamba a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya ce ziyarar tana da muhimmiyar ma'ana ta tarihi, wanda ke nuna wani sabon matsayi a dangantakar dake tsakanin jam'iyyun biyu da ma kasashen. (Ibrahim)