logo

HAUSA

Adadin Kudin Shiga Na Yawon Bude Ido Na Cikin Gida Na Kasar Sin Ya Karu Da 114% A Watanni 9 Na Farkon Bana

2023-12-14 19:49:23 CMG Hausa

Babban jami'in kula da harkokin al'adu da yawon bude ido na kasar Sin, ya bayyana cewa, kasuwar yawon shakatawa ta kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba a cikin watanni 9 na farkon bana.

Alkaluman da ma'aikatar al'adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, yawan masu yawon bude ido na cikin gida ya kai biliyan 3.67, yayin da kudin shigar da aka samu a wannan lokaci, ya kai kudin Sin RMB yuan triliyan 3.7, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 520.47, wanda ya nuna karuwar kashi 75 cikin 100 da kashi 114 bisa 100 bi da bi bisa makamancin lokaci na bara.

Mataimakin ministan al'adu da yawon bude ido na kasar Sin Du Jiang, ya ce karuwar sha'awar tafiye-tafiye a tsakanin mazauna a wannan shekara, ta sa bunkasar harkar yawon shakatawa na cikin gida sosai.(Ibrahim)