logo

HAUSA

Sin: in Amurka ta kara sa ido ga sauran kasashe, za ta rasa karin abokai

2023-12-14 20:14:47 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, gwamnatin kasar Amurka tana kara sa ido da tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe da ma harkokin duniya, wannan hanya ta saba wa dokokin kasa da kasa da tsarin da ake bi wajen yin hadin gwiwa da kasashen duniya. Idan Amurka ta ci gaba da sa ido kan sauran kasashe, hakika za ta rasa karin abokai.

Dangane da bayanin da sojojin Koriya ta Kudu suka yi na cewa, jiragen yakin kasar Sin 2 da na Rasha 4 sun shiga yankin tantance tsaron sararin samaniyar Koriya ta Kudu a yau din nan. Mao Ning ta ce, wannan wani aiki ne na yau da kullum da jiragen yakin kasar Sin ke yi a sararin samaniyar kasa da kasa, kuma ya dace da dokokin kasa da kasa.

A wannan rana, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Zhang Xiaogang ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, yankin Taiwan yanki ne na kasar Sin da ba a iya raba shi ba. Kasar Amurka ta mai da mashigin tekun Taiwan a matsayin yankin teku na kasa da kasa don tsoma baki a batun yankin Taiwan, da kawo barazana ga ikon mallakar kasar Sin. Kuma Sin tana adawa da wannan batu.

Hakazalika kakakin ya ce, har kullum kasar Sin tana ba da shawarar yin amfani da sararin samaniya cikin lumana, da sa kaimi ga hadin gwiwar kasa da kasa a fannin sararin samaniya, da yin adawa da amfani da makamai a sararin samaniya. (Zainab)