logo

HAUSA

Manzon musamman na shugaban kasar Sin zai halarci bikin rantsar da shugaban Madagascar

2023-12-13 20:07:20 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau cewa, bisa gayyatar da shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina ya yi masa, manzon musamman na shugaban kasar Sin kuma mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Hu Chunhua, zai halarci bikin rantsar da shugaban kasar Madagascar da za a yi a babban birnin kasar wato birnin Tananarive a ranar 16 ga wannan wata.

Game da kudurin da babban taron MDD ya zartas na neman tsagaita bude wuta a zirin Gaza, Mao Ning ta bayyana cewa, Sin ta nuna goyon baya ga wannan kuduri, da fatan za a aiwatar da kudurin a dukkan fannoni don cimma burin tsagaita bude wuta cikin hanzari.

Game da dangantakar tattalin arziki a tsakanin Sin da Amurka, Mao Ning ta bayyana cewa, tushen hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen biyu shi ne samun moriyar juna. Ya kamata Amurka ta girmama ka’idojin tattalin arzikin kasuwanci da na cinikayyar duniya, don samar da kyakkyawan yanayin yin hadin gwiwarsu a wannan fanni.

Ban da wannan kuma, ma’aikatar harkokin ciniki ta kasar Sin ta mayar da martani game da matakin Amurka na shigar da kamfanonin Sin uku a cikin jerin sunayen kamfanonin da ake kira "Dokar hana aikin tilastawa ta Uygur", inda kasar Sin ta bayyana cewa tana adawa da aikin tilas. Babu wani abin da ake kira "aikin tilastawa" a jihar Xinjiang kwata-kwata. Kasar Sin ba ta gamsu da matakin Amurka ba, kuma tana adawa da hakan. (Zainab)