logo

HAUSA

Shugaba Xi ya gana da manyan shugabannin kasar Vietnam

2023-12-13 14:02:55 CMG Hausa

A safiyar yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda yake ziyara a kasar Vietnam, ya gana da takwaransa na kasar Vietnam Vo Van Thuong, a Hanoi, fadar mulkin kasar ta Vietnam.

Yayin ganawar tasu, Xi Jinping ya ce, wannan shi ne karo na uku da ya kai ziyarar aiki kasar Vietnam, tun bayan da ya kama aiki a matsayin shugaban kasa, kuma babban sakataren kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin. Kana, wannan ita ce ziyarar da ya kai kasar tun bayan ziyarar aikin da babban sakataren na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Vietnam Nguyen Phu Trong ya kai ga kasar Sin a watan Oktoban bara, kuma, ziyarar aiki da za ta kasance ta karshe da zai kai wata kasar waje a bana. Lamarin da ya nuna muhimmin matsayin huldar diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da Vietnam, cikin dangantakar diflomasiyya mai wanzuwa tsakanin kasar Sin da kasashen waje, musamman ma a tsakaninta da kasashe makwabta.

Ya kuma kara da cewa, “Yanzu muna kan wani sabon mafari, kuma kasar Sin tana son karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, wajen zurfafa mu’amalar dake tsakaninsu, domin inganta dunkulewar al’ummomin kasashen Sin da Vietnam, wanda hakan ke da muhimmiyar ma’ana, ta yadda sassa biyu za su tallafa wa al’ummominsu yadda suke fata.

A yau da safe dai, shugaba Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Vietnam Pham Minh Chinh, da shugaban majalisar dokokin kasar Vuong Dinh Hue a birnin Hanoi. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)