logo

HAUSA

Madam Peng Liyuan da uwargidan shugaban kasar Vietnam sun ziyarci Jami’ar Hanoi

2023-12-13 14:37:20 CMG Hausa

Da safiyar yau Laraba 13 ga wata bisa agogon wurin, Madam Peng Liyuan, uwargidan shugaban kasar Sin Xi Jinping, ta ziyarci Jami’ar Hanoi, bisa rakiyar da Madam Phan Thi Thanh Tam, uwargidan shugaban kasar Vietnam Võ Văn Thưởng ta yi mata.

Madam Peng ta saurari bayanin da aka gabatar kan yadda aka kafa jami’ar, da tafiyar da harkokinta, da ma yin mu’amala a tsakanin jami’ar da sauran kasashe, inda ta nuna fatanta na ganin yadda bangarorin biyu za su kara yin hadin gwiwa, da cudanyar aikin koyarwa a tsakaninsu, tare da maraba da matasan kasar Vietnam da su je kasar Sin don karo ilminsu, ta yadda za a kara fahimta, da zumunci a tsakanin bangarorin biyu.  (Kande Gao)