logo

HAUSA

Ina Tattalin Arzikin Sin Ya Dosa? Babban Taron Aikin Raya Tattalin Arziki Ya Ba Da Amsa

2023-12-13 20:20:50 CMG Hausa

Taron kolin raya tattalin arzikin kasar Sin da ake gudanarwa a karshen ko wace shekara, wata muhimmiyar kafa ce ga jama'ar cikin gida da ketare, na lura da alkiblar da tattalin arzikin kasar Sin ya sanya gaba. Kuma kamar yadda aka tsara yi daga ranar 11 zuwa 12 ga watan Disamba ne, aka gudanar da babban taron koli na aikin raya tattalin arziki a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Hukunce-hukuncen da aka yanke a wannan taro shi ne cewa, ci gaban kasar Sin yana fuskantar yanayi mai kyau fiye da abubuwan dake iya kawo cikas, kuma yanayin farfadowar tattalin arziki da inganci na dogon lokaci bai sauya ba. Kuma tilas ne a kara nuna tabbaci.

Haka kuma babban taron ya yi wani tsari na musamman, da fito da wasu muhimman fannonin aikin raya tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2024. Babban aikin shi ne, sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki mai inganci, ciki har da karfafa sabbin masana'antu, da mai da hankali kan fadada bukatun cikin gida, da kara kudin shiga na mazauna birane da yankunan karkara, da inganta ci gaban kamfanoni masu zaman kansu, da dai sauransu.(Ibrahim)