logo

HAUSA

Hasashen Airbus: Sin za ta kasance babbar kasuwar hidimomin sufurin sama zuwa shekarar 2042

2023-12-13 10:52:42 CMG

Wani hasashe na kamfanin kirar jiragen sama na Airbus, ya nuna cewa ya zuwa shekarar 2042, kasar Sin za ta kasance a sahun gaba, a jerin kasashen duniya a fannin samar da hidimomin sufurin jiragen sama, inda kasuwar ta a fannin za ta daga zuwa dalar Amurka biliyan 54.1.

Hasashen na kamfanin Airbus ya nuna cewa, Sin za ta zarce nahiyar Turai da arewacin Amurka, a karfin kasuwar sufurin jiragen sama, yayin da take kara fadada hada hadar sufurin kamfanonin jiragen saman kasuwa na cikin gida, wadda ka iya bunkasa zuwa 10,930 nan da shekarar ta 2042.

Yayin da kasar ta Sin ke kara daidaita ci gaban ta a fannin cimma nasarar burikan ta guda 2, game da dakile illar iskar carbon mai dumama yanayi, sashen sufurin saman kasar yana kara inganta, kana hidimomin da yake samarwa ma na kara kyautata.

Har ila yau, kasar na kara samar da damammaki ga kasuwar bayar da hidimomi a manyan sassa 3, wadanda suka hada da lura da na’urori, da bayar da horo da gudanarwa, da kuma fannin kyautata jin dadin fisinjoji.   (Saminu Alhassan)