logo

HAUSA

Xi Jinping da babban sakataren JKV sun gana da wakilan matasa da masu sada zumunta na kasashen biyu

2023-12-13 20:33:31 CMG Hausa

A yammacin yau ne, shugaban kasar Sin kuma babban sakataren JKS Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan da babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Vietnam Nguyen Phu Trong da mai dakinsa suka gana da wakilan matasa da masu sada zumunta na kasashen biyu.

Yayin da shugaba Xi da uwargidansa Peng suke shirin dawowa gida bayan kammala ziyarar aiki a Vietnam, sun yi ban kwana da babban sakatare Nguyen Phu Trong da mai dakinsa. (Zainab)