logo

HAUSA

Xi Ya Gana Da Babban Sakataren Kwamitin Kolin JKV

2023-12-12 19:20:29 CMG Hausa

Babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana yau Talata cewa, tare da kokarin hadin gwiwa, huldar dake tsakanin kasashen Sin da Vietnam za ta shiga wani sabon mataki na amincewa da juna a fannin siyasa, da karin hadin gwiwa a fannin tsaro, da zurfafa hadin gwiwar moriyar juna da goyon baya mai karfi, da zurfafa cudanyar bangarori daban daban, da sarrafa bambance-bambance yadda ya kamata.

A yayin ganawarsa da babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Vietnam Nguyen Phu Trong a yau, shugaba Xi ya bayyana cewa, manufar gina tsarin gurguzu a kasashen Sin da Vietnam, za ta ci gaba da ba da gudummawa sosai wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba da wadata a yankin, da ma duniya baki daya. (Ibrahim Yaya)