logo

HAUSA

Yawan Yankunan Raya Fasahar Zamani Na Kasar Sin Ya Karu Zuwa 178

2023-12-12 19:30:13 CMG Hausa

Mataimakin daraktan sashen tsare-tsare na ma'aikatar masana'antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin Wu Jiaxi ya bayyana cewa, ya zuwa karshen watan Nuwamba, yawan yankunan raya fasahar zamani ya kai 178.

Wu Jiaxi ya bayyana cewa, a watanni tara na farko na wannan shekarar da muke ciki, yawan karuwar tattalin arzikin wadannan yankunan raya fasahar zamani, ya kai kudin Sin RMB yuan triliyan 12.33, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 1.73, wanda ya karu da kashi 7.11 cikin 100 kan na makamancin lokaci na shekarar da ta gabata.(Ibrahim)