logo

HAUSA

Xi ya isa Vietnam domin gudanar da ziyarar aiki

2023-12-12 13:48:56 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya isa kasar Vietnam, domin fara ziyarar aiki ta yini biyu, inda ake sa ran yayin ziyarar ta sa, sassan biyu za su tattauna matakan daga matsayin dangantakar su, da tsara dabarun zurfafawa, da karfafa hadin gwiwarsu bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni.

A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, shugaba Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, ya samu babbar tarba ta karramawa a Vietnam, inda aka shimfida masa jar dardumar maraba da zuwa.  (Saminu Alhassan)