logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a kauracewa tsoma hannu cikin harkokin gidan DRC

2023-12-12 11:06:47 CMG Hausa

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira ga sassan kasa da kasa da su kauracewa tsoma hannu cikin harkokin gidan janhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC. Dai Bing ya yi wannan kira ne a jiya Litinin, yayin da ake tattauna batutuwan da suka shafi kasar a zauren kwamitin tsaron MDD.

Ya ce janhuriyar dimokaradiyyar Congo, na cikin wani muhimmin lokaci na raya tsarin siyasa, da tabbatar da tsaro da daidaito, kuma idan kasar ta cimma nasarar wanzar da zaman lafiya, daidaito da ci gaba, hakan zai haifar da alfanu ga al’ummun kasashen dake shiyyar ta, da ma sauran al’ummun kasa da kasa.

Dai Bing, ya ce zaben janhuriyar dimokaradiyyar Congo na karatowa. Kuma Sin na jinjinawa kokarin gwamnati da hukumar zaben kasar a fannin shirya sahihin zabe. Kaza lika Sin na da imanin cewa, gwamnati da jama’ar janhuriyar dimokaradiyyar Congo na da ikon gudanar da zabe cikin lumana.

Ya ce zabe harkar cikin gida ce ta janhuriyar dimokaradiyyar Congo, don haka ya dace sassan kasa da kasa su martaba ikon mulkin kai, da jagorancin kasar, su karfafa gwiwar dukkanin sassa, ta yadda za a kai ga warware sabani ta hanyar tattaunawa da shawarwari, kana su kauracewa tsoma baki cikin harkokin kasar na cikin gida. (Saminu Alhassan)