logo

HAUSA

Matsayi guda biyar na kasar Sin wajen tunkarar kalubalen sauyin yanayi

2023-12-12 13:45:28 CMG Hausa

A yayin babban taron kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD, karo 28 wato COP28 da ake gudanar a birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa, shugaban kungiyar kasa da kasa ta lura da yanayi ko WMO, Abdulla Ahmed Al Mandous ya bayyana cewa, kasar Sin tana tunkarar kalubalen sauyin yanayi yadda ya kamata, kana tana bin hanya mafi dacewa ta shawo kan kalubalen.

Al Mandous ya kara da cewa, a ko da yaushe, kasar Sin tana inganta ayyukan kare yanayi na kasashen duniya bisa matsayinta a bangarori biyar, kuma kokarin da take yi na samun amincewa daga bangarori daban daban, lamarin da ya sa ta ba da gudummawa sosai ga kara karfin COP28.

Matsayin kasar na farko shi ne, kasancewar ta muhimmiyar mamba a jerin kasashe masu tasowa.

Alkaluman da bankin duniya ya fitar sun nuna cewa, a shekarar 2022, matsakaicin ma’aunin tattalin arzikin GDP na ko wane Basine ya kai dallar Amurka 12,720, adadin da ya kai kaso 1 bisa 6 da ake da shi a kasar Amurka, kuma daidai da kaso 1 bisa 4 da ake da shi a kasar Jamus, ko kaso 1 bisa 3 na wanda ake da shi a kasashe mambobin kungiyar tarayyar Turai wato EU, Kuma da hakan, kasar Sin ta kasance a matsayi na 67, cikin kasashen duniya a wannan fanni.

Haka kuma, matsakaicin ma’aunin tattalin arzikin GNI, na ko wane Basine ya kai dallar Amurka 12850, adadin da ya kai matsayi na 62 tsakanin kasashen duniya. Hakan ya sa, kasar Sin ta kai matsayin kasa mai tasowa mafi girma tsakanin kasashen duniya.

Matsayin kasar Sin na biyu shi ne, kasa mai samun saurin raya tattalin arziki, wadda ba ta sauya daga sauke nauyin da aka dora mata a tarihi ba. Idan muka duba jimillar hayaki mai dumama yanayin duniyarmu da kasashen duniya suka fitar a baya, za mu ga cewa, daga shekarar 1850 zuwa shekarar 2019, adadin hayaki mai dumama yanayi da kasashen dake nahiyar arewacin Amurka suka fitar ya kai kaso 23 bisa dari na jimillar kasashen duniya, kuma, yawan hayaki mai dumama yanayin duniyarmu da kasashen Turai suka fitar ya kai kaso 16 bisa dari na kasashen duniya. Amma a yanzu, yawan hayaki mai dumama yanayi da kasar Sin ke fitarwa bai wuce kashi 1 bisa 8 din na kasar Amurka ba, ko kashi 1 bisa 4 na gamayyar kasashen kungiyar EU. Shi ya sa, nauyin da kasar Sin ta dauka bai canja ba. A yanzu, kasar Sin tana dukufa wajen fuskantar kalubalen sauyin yanayi.

Matsayin kasar Sin na uku shi ne, kasancewa mai ba da gudummawar raya sabbin makamashi.

Cikin dogon lokacin da ya gabata, kasar Sin ta dukufa wajen raya makamashi mai tsafta, yayin da take kyautata tsarin samar da makamashin baki daya. A shekarar 2022, yawan kwal da kasar Sin ta yi amfani da shi ya ragu, daga kaso 66 bisa dari na shekarar 2015 zuwa kaso 56 bisa dari. Kuma, ya zuwa watan Oktoba na shekarar 2023, yawan lantarki da kasar Sin ta samar ta hanyar amfani da makamashi mai tsabta, ya zarce kilowatt biliyan 1 da miliyan dari 4. Adadin da ya kai kaso 49.9 bisa dari na yawan lantarki da kasar ta samar gaba daya, lamarin da ya sa kasar Sin ta kasance a matsayin farko a wannan fanni a duk fadin duniya.

Matsayin kasar Sin na hudu shi ne, kasa mai neman daidaito a tsakanin aikin raya tattalin arziki da kare muhalli.

Tun daga shekarar 2013 zuwa yanzu, kasar Sin ta cimma nasarar kona makamashin da karuwarsu ta kai kaso 3 bisa dari don samun karuwar tattalin arziki na kaso 6.2 bisa dari a ko wace shekara, ta kuma cimma nasarar raya tattalin arziki ta hanyar kare muhalli, yayin da take tabbatar da samun isassun makamashi da hatsi, tare da kare yanayi da muhallin halittu.

Matsayin kasar Sin na biyar shi ne, kasa mai raya ayyukan daidaita muhallin kasashen duniya bisa fannoni daban daban.

A matsayin babbar kasa dake cikin jerin kasashe masu tasowa, kasar Sin tana dukufa wajen raya hadin gwiwar kasashe masu tasowa, domin fuskantar sauyin yanayi, inda har ta bayar da kwas din horaswa kan hadin gwiwar kasashe masu tasowa wajen fuskantar sauyin yanayi sau 57, kana ta ba da horo ga dalibai sama da dubu 4 daga kasashe kimanin dari 1, domin ba da taimako ga kasashe masu tasowa ta fuskantar sauyin yanayi, da kuma ba da gudummawar cimma burin neman dauwamammen ci gaba na MDD nan zuwa shekarar 2030. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)