logo

HAUSA

Ministocin wajen Sin da Iran sun tattauna game da batun Gaza

2023-12-12 10:03:05 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin, kuma memba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS Wang Yi, ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Iran Hossein Amir-Abdollahian, game da yanayin da ake ciki a zirin Gaza.

Yayin tattaunawar ta su a jiya Litinin, mista Wang ya yi bitar matsayar Sin game da halin da ake ciki a Gaza, yana mai cewa, Sin na fatan ganin an cimma nasarar tsagaita wuta, da gaggauta kawo karshen tashin hankali, kana da tabbatar da samar da agajin jin kai, da dora muhimmanci kan kafuwar kasashe biyu.

Wang ya kara da cewa, Sin a shirye take da ta aiwatar da muhimmin matsayin da shugaba Xi Jinping da takwaransa na Iran Ebrahim Raisi suka cimma, yayin ganawa biyu da suka yi a bana, kana Sin na yin duk mai yiwuwa, wajen ingiza ci gaban dangantakar kasashen 2 zuwa wani sabon matsayi.

Kaza lika a cewar mista Wang, Sin na goyon bayan aniyar kasashen Iran da Saudiyya, a yunkurin su na kara bunkasa dangantaka, da yayata dunkulewa, da hadin gwiwar kasashen dake yankin su, tare da rike ragamar wanzar da zaman lafiya da tsaron yankin a hannun su. (Saminu Alhassan)