logo

HAUSA

Hamas: Ba za a yi musayar mutanen da ake tsare da su da Isra’ila kafin a yi cikakken tsagaita wuta a zirin Gaza ba

2023-12-12 12:25:20 CMG Hausa

Babban jami’in Hamas Osama Hamdan ya bayyana yayin tattaunawa da gidan talabijin na Qatar Penninsula a daren jiya Litinin cewa, ba za a yi musayar mutanen da ake tsare da su da Isra’ila kafin a yi cikakken tsagaita wuta a zirin Gaza ba.

Wasu kafofin watsa labarai na Isra’ila sun rawaito cewa, bangaren Isra’ila ya riga ya sanar wa kasashe masu shiga tsakani, ciki har da Qatar da Masar, cewar yana fatan gudanar da sabuwar tattaunawa game da musayar mutane da aka tsare ta hanyar tsagaita wuta domin agajin jin kai. Game da wannan, Hamdan ya ba da amsa cewa, ba za a tattauna wannan batu ba har sai sojojin Isra’ila sun daina kai hari kan zirin Gaza.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta zirin Gaza ta fitar da sanarwa a jiya Litinin cewa, tun barkewar sabon rikici tsakanin Falasdinu da Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, ayyukan soja da sojojin Isra’ila suka gudanar a zirin Gaza sun haddasa mutuwar Falasdinawa fiye da 18,200, yayin da fiye da dubu 49 suka ji raunuka. (Safiyah Ma)