logo

HAUSA

(COP28) Shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kasashe masu arziki da su cika alkawuran magance sauyin yanayi

2023-12-12 10:56:46 CMG Hausa

A jiya Litinin ne sakatare-janar na MDD Antonio Guterres ya bukaci kasashe masu arziki da su cika alkawuran da suka dauka na magance sauyin yanayi.

Sakatare-janar na MDD ya kuma yi kira da a hada kai tsakanin bangarori daban daban domin tunkarar wannan kalubale na bai daya dake addabar Bil’adama. “A duniyarmu daka cike da rarrabuwar kawuna, COP28 ya kasance kyakkyawar kafar tunkarar kalubalen duniya ta hanyar la’akari da ra’ayin bangarori daban daban,” a cewarsa.

Sakataren zartaswar sauyin yanayi na MDD Simon Stiell a ranar Litinin ya yi kira ga dukkan bangarorin da suka hada kai don cimma matsaya na karshe na taron.

Babban jami'in sauyin yanayi na MDD ya ce har yanzu akwai sauran  muhawara kan muhimman batutuwa guda biyu: Burin kasashe kan batun dakile matsalar sauyin yanayi da kuma niyyarsu ta karfafa burin mika mulki tare da hanyoyin tallafi da suka dace.

Ya yi nuni da cewa "'Na yi nasara, kai ka fadi shi ne matakin gazawa ta gama gari," ya yi kira da a kawar da shingen dabarun da ba a bukata, da habaka manufa, da kuma mutunta matsayin kowace kasa, ta hanyar tabbatar da muhimman ka'idoji da wakilci, da nuna gaskiya, da kuma sanya buri mafi girman a gaba.

Shugaban COP28 Sultan Ahmed Al Jaber ya sanar a ranar Litinin da amincewa da shawarar gudanar da COP29 a Azerbaijan. (Yahaya)