logo

HAUSA

Xi Jinping ya wallafa makala a jaridar Nhan Dan ta kasar Vietnam

2023-12-12 11:12:28 CMG Hausa

Yayin da ya kai ziyarar aiki birnin Hanoi, babban birnin kasar Vietnam, babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kasar Xi Jinping, ya wallafa wata makala mai dauke da sunansa a jaridar Nhan Dan ta kasar Vietnam. Taken makalar ta shugaba Xi shi ne “Gina al’umma mai makomar bai daya ta Sin da Vietnam mai ma’ana bisa manyan tsare-tsare, da bude sabon babin neman zamanantarwa tare”.

Wannan ne karo na uku da Xi Jinping ke kai ziyarar aiki kasar Vietnam a matsayin shugaban koli na JKS da na kasar Sin. Cikin makalar tasa, ya bayyana cewa, a ko da yaushe jam’iyyar kwaminis da gwamnati na Sin, suna daukar bunkasa dangantakar Sin da Vietnam a matsayin abu mai muhimmanci, yayin da Sin take kulla dangantakar diplomassiya tare da kasashe makwabta. 

Kaza lika shugaban na Sin, ya yi fatan kasashen biyu ba za su manta da ainihin abota ta gargajiya tsakaninsu ba, kana su kiyaye akidu da manufa guda, su yi tafiya a kan hanyar gurguzu tare, da kuma ci gaba da inganta gina al'umma mai kyakkyawar makomar bai daya dake da ma’ana bisa manyan tsare-tsare.

Xi Jinping ya ba da shawarar cewa, ya kamata kasashen Sin da Vietnam su ci gaba da yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da yin amfani da karfin juna, da karfafa mu'amalar abokantaka, da sarrafa bambance bambancen teku yadda ya kamata, da samar da hanyoyin da za a amince da su tare. 

Ya ce Sin za ta ci gaba da tabbatar da dorewa, da kwanciyar hankali a manufofinta na raya dangantakar diplomassiyar kasashe makwabta, da tsayawa tsayin daka kan bin ka’idoji na samun kyautatuwa, da abokantaka, da kuma wadata tare da kasashe makwabta. 

A sa'i daya kuma, za ta ba da sabuwar ma'ana ga manufar son juna da kare moriyar juna, da sanya zamanantarwa irin ta kasar Sin ta kara haifar da fa'ida ga kasashe makwabta, tare da inganta tsarin zamanantarwa ga kasashen Asiya, da samar da sabbin damamakin samun ci gaba ga kasashen Asiya ciki har da Vietnam. (Safiyah Ma)