logo

HAUSA

Kokarin Sin Wajen Kawar Da Gurbatar Iska Ya Janyo Jarin Da Ya Kai Yuan Triliyan 4

2023-12-11 20:04:32 CMG Hausa

Ma'aikatar kula da muhalli ta kasar Sin ta sanar da cewa, an samu gagarumin ci gaba, a kokarin da ake na dakile gurbatar iska a cikin 'yan shekarun baya-bayan nan, matakin da ya haifar da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.

Babban injiniya a ma'aikatar Liu Bingjiang ya shaidawa taron manema labarai yau Litinin cewa, ci gaban da kasar Sin take samu kan kyautata ingancin iska, yana tafiya cikin sauri a duniya, yayin da aka warware matsalar gurbatar yanayi a sanadiyar makamashin kwal a fadin kasar.

Ya bayyana cewa, kokarin kasar Sin na dakile gurbatar iska, ya janyowa kasar jarin da ya kai kudin Sin RMB Yuan triliyan 4, kimanin dalar Amurka biliyan 562.09, baya ga bunkasar GDPn kasar da kusan Yuan triliyan 5.(Ibrahim)