logo

HAUSA

An watsa kashi na biyu na shirin “labarun da Xi Jinping ya fi so” a Vietnam

2023-12-11 19:05:11 CMG Hausa

 

A gabanin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai kasar Vietnam, yau Litinin din nan aka watsa kashi na biyu na shirin telebijin na "Labarun da Xi Jinping ya fi so", wanda babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya shirya a Vietnam.

A yayin bikin da aka gudanar a birnin Hanoi na Vietnam a wannan rana, shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.

Haka kuma a wannan rana, an gudanar da bikin kaddamar da sabon zagaye na hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labaru na kasashen Sin da Vietnam a birnin Hanoi na Vietnam, inda kuma Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. (Ibrahim)