logo

HAUSA

An yi nasarar gudanar da zaben ’yan majalisar kafa dokoki ta yankin Hong Kong karo na 7

2023-12-11 11:30:55 CMG Hausa

An cimma nasarar gudanar da zaben ’yan majalisar kafa dokoki ta yankin Hong Kong karo na 7. Shi ne zaben ’yan majalisar kafa dokoki ta yankin karo na farko, tun bayan aiwatar da manufar "tabbatar da ’yan kishin kasa su yi mulkin yankin Hong Kong", da kuma sake fasalin tsarin majalisar kafa dokokin yankin. Ana ganin cewa, Hong Kong ta dauki wani kwakkwaran mataki, na gudanar da harkokin yanki yadda ya kamata.

A yayin zaben, an zabi mambobin kwamitocin gundumomin mazabu 176, da kuma kansilolin mazabu 88. (Mai fassara: Bilkisu Xin)