logo

HAUSA

Sin Ta Jagoranci Kaddamar Da Shirin Aiwatar Da "Tsarin Kunming-Montreal" A Taron Sauyin Yanayi Na MDD A Hukumance

2023-12-10 16:27:30 CMG Hausa

A ranar 9 ga wata bisa agogon wurin, yayin biki mai taken "Natural Day" na babban taron kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo 28 COP28 da ake gudanar a birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa, kasar Sin ta sanar da shiga kungiyar “ High Ambition Alliance for Nature and Humanity" a hukumance, inda ta jagoranci kaddamar da shirin aiki na "Kunming-Montreal Global Diversity Framework".

A yayin bikin, shugaban babban taron sassan da suka amince da yarjejeniyar kare mabambantan halittu karo na 15, kuma ministan kula da muhalli na kasar Sin, Huang Runqiu ya bayyana ta kafar bidiyo cewa, matsalar sauyin yanayi da yadda ake asarar mabambantan halittu, suna haifar da babban kalubale ga rayuwa da ma ci gaban bil-Adama. Kasar Sin na fatan babban taron na COP28, zai aiwatar da hadin gwiwa tsakanin bangarori da dama bisa gaskiya, tare da samun sakamako mai kyau da kuma inganci.

Huang Runqiu ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin da su gaggauta yin kwaskwarima ga “manyan tsare-tsare da shirin ayyukan kiyaye mabambantan halittu”, da kuma tattara karin albarkatu, don kara azama kan cimma manyan manufofi guda uku na yarjejeniyar kare mabambantan halittu bisa daidaito.

Kasar Sin tana maraba da dukkan masu ruwa da tsaki, da su taka rawar gani wajen gudanar da harkokin kula da mabambantan halittu, kuma tana matukar yabawa da goyon bayan dukkan alkawura da tsare-tsare da hadin gwiwar da suka dace, wajen sa kaimi ga aiwatar da tsarin aikin Kunming-Montreal.

Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya, wajen tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta kamar hasarar rabe-raben halittu da matsalar sauyin yanayi, tare da sa kaimi ga cimma nasarar gudanar da babban taron bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 28 COP28, domin samar da duniya mai kyau inda za a samu zaman jituwa tsakanin mutum da yanayi. (Ibrahim)