logo

HAUSA

Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba

2023-12-10 16:16:06 CMG Hausa

A yayin taron manema labaru na farko da tawagar kasar Sin mai halartar babban taron kasashen duniya da suka sanya hannu kan yarjejeniyar MDD kan sauyin yanayi karo na 28 COP28 ta gudanar a jiya, manzon musamman mai kula da harkokin sauyin yanayi na kasar Sin Xie Zhenhua ya yi bayani game da nasarorin da Sin ta samu wajen canja tsarin raya kasa tare da kiyaye muhalli da raya makamashin da za a iya sabuntawa. Xie ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasa da kasa wajen tinkarar sauyin yanayi.

Xie Zhenhua ya bayyana cewa, kasar Sin ta samar da babbar gudummawa wajen kyautata tsarin samar da makamashi da raya makamashin da za a iya sabuntawa. Ya zuwa yanzu, yawan kudin da aka kashe wajen samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da karfin iska ya ragu da kashi 80 cikin dari, yawansu ta hanyar hasken rana ya ragu da kashi 90 cikin dari, wadanda suka aza tubalin yin amfani da irin wannan makamashi a fadin duniya. A halin yanzu, yawan na’urorin samar da makamashin da za a sabuntawa ya fi yawan na kwal, wannan wani babban canji ne a tsarin samar da makamashi. Sin za ta ci gaba da yin amfani da makamashin da za a iya sabuntawa don maye gurbin makamashin kwal da sauran burbushin halittu.

Wakilin Sin ya kara da cewa, Sin ta hada kai da kasashe da yankuna fiye da 100, kan ayyukan samar da makamashi masu tsabta, da daddale yarjejeniyoyin fahimtar juna kan hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa wajen tinkarar sauyin yanayi tare da kasashe masu tasowa fiye da 10. A nan gaba Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasashe masu tasowa don inganta hadin gwiwarsu a fannonin kudi da fasahohi. (Zainab)