logo

HAUSA

Jiragen ruwan Philippines sun yi karo da jirgin ruwan ‘yan sandan tekun Sin da gangan

2023-12-10 16:35:46 CMG Hausa

A yau ne, jiragen ruwan ‘yan sandan tekun Philippines guda 2, da jirgin ruwan aikin kasar guda daya, da jirgin ruwan dakon kayayyaki guda daya suka kutsa cikin yankin tekun dake kusa da tsibirin Ren’ai na yankin tsibiran Nansha na kasar Sin ba tare da samun iznin gwamnatin kasar Sin ba. Sai dai jami’an tsaron gabar tekun kasar Sin sun dauki matakan shawo kan jiragen ruwan na Philippines. Bayan haka, wani jirgin ruwan kasar Philippines ya keta ka’idojin kasa da kasa na hana tashe-tashen hankula a kan teku, inda ya juya ba zato ba tsammani, ya kuma yi karo da jirgin ruwan ‘yan sandan tekun kasar Sin mai lamba 21556 da gangan, inda ya gogi jirgin ruwan, ya kamata bangaren Philippines ya dauki alhakin wannan batu. (Zainab)