logo

HAUSA

Hangzhou: An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Kan Shirye-shiryen Rediyo Da Telebijin Karo Na 6

2023-12-10 20:23:56 CMG Hausa

Yau Lahadi ne aka gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa kan shirye-shiryen rediyo da telebijin karo na 6 a birnin Hangzhou da ke gabashin kasar Sin, inda Li Shulei, mamban hukumar siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya halarci bikin bude taron tare da gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.

Mahalarta taron suna ganin cewa, kamata ya yi kafofin yada labaru na kasar Sin da kasashen Larabawa, su kara daukar managartan matakai da za su taimaka wajen karfafa zumunci tsakanin Sin da kasashen Larabawa, a kokarin kara ba da gudummowa wajen kara azama kan ci gaban bangarorin 2 da wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankuna da ma duniya baki daya. (Tasallah Yuan)