logo

HAUSA

Kasar Sin za ta daukewa wasu kasashen Afirka 6 harajin kwastan kan kaso 98 bisa dari na hajojin da suke shigarwa kasar

2023-12-08 14:06:23 CMG Hausa

Kwanan baya, kwamitin kula da ka’idojin harajin kwastan na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fidda da wata sanarwa, wadda ke cewa bisa musayar takardun da gwamnatin kasar Sin ta yi da gwamnatocin wasu kasashe 6, tun daga ranar 25 ga watan Disamba na bana, Sin din za ta daina karbar harajin kwastan kan kaso 98 bisa dari na hajojin da suke shigarwa kasar Sin.

Kasashen da wannan rangwame ya shafa, kasashe ne masu raunin tattalin arziki, da suka hada da kasar Angola, da Gambia da Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo, da Madagascar da Mali da kuma kasar Mauritania. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)