logo

HAUSA

Sin: Ya kamata kwamitin sulhu ya kara daukar matakai kan lokaci don inganta tsagaita bude wuta da kawo karshen yaki a dukkan fannoni

2023-12-08 20:47:40 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce ya kamata kwamitin sulhun na MDD, ya kara daukar matakan da suka dace a kan lokaci, don sa kaimi ga tsagaita bude wuta, da kawo karshen yaki a dukkan fannoni, kana da kare fararen hula yadda ya kamata, da kuma sassauta yanayin jin kai.

Jami’in ya bayyana haka ne a yau Jumma’a, a yayin da yake ba da amsa kan bukatar da sakatare-janar na MDD António Guterres ya gabatarwa kwamitin sulhun, game da daukar matakai kan halin da ake ciki a zirin Gaza, bisa aya ta 99 dake kunshe cikin kundin tsarin mulkin majalisar.

Baya ga haka, jami’in ya jaddada cewa, kamata ya yi kwamitin sulhun ya saurari muryoyin kasashen Larabawa, da na Musulunci, da kuma na kasa da kasa. Ya ce kasar Sin na goyon bayan kokarin shiga tsakani na sakatare-Janar da sakatariyar MDD, za kuma ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa tare da bangarorin da abin ya shafa, da kuma taka rawa mai ma'ana wajen sa kaimi ga kwantar da tarzoma.

Sakatare-Janar António Guterres, ya rubuta wasika zuwa ga shugaban kwamitin sulhun na wannan karo, inda ya bayyana cewa, halin da ake ciki a Gaza na iya zama barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, ya kuma bukaci kwamitin sulhun da ya dauki matakan inganta tsagaita bude wuta na jin kai, da kuma kaucewa bala'in jin kai. Wannan dai shi ne karo na farko cikin shekaru sama da 50, da sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi amfani da aya ta 99, ta kundin tsarin mulkin MDD. (Mai fassara: Bilkisu Xin)